in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan tana fatan Amurka za ta soke takunkumin da ta sa mata kamar yadda aka tsara
2017-06-28 15:45:53 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sudan Abdul-Ghani Al-Naeem ya bayyana a jiya cewa, kasarsa na fatan bayan kasar Amurka ta fara aiwatar da shirin hana ci rani, lamarin ba zai kawo barazana ga soke mata takunkumi kamar yadda aka tsara aiwatarwa a hukumance cikin watan Yuli mai zuwa ba.

Bugu da kari, Mr.Naeem ya jaddada cewa, a halin yanzu, akwai hadin gwiwa tsakanin kasashen Sudan da Amurka, kuma ana gudanar da shi cikin yanayi mai kyau, musamman ma a fannonin yaki da ta'addanci, da kuma hana fataucin bil adama.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China