A jawabinta yayin bikin bude taron, ministar albarkatun ruwa ta kasar Morocco Charafat Afilal ta bayyana cewa, idan har aka bunkasa bangaren samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa, hakika zai kasance wata mahimmiyar kafa da nahiyar za ta yi amfani da ita wajen inganta rayuwar al'ummominta.
Afilal ta ce nahiyar ba ta ci gajiyar da kaso 14 cikin 100 na wutan lantarkin da ake samu daga karfin ruwa a duniya, kuma nahiyar ta Afirka za ta iya samun gigawatts 300 na hasken wutan lantarki daga wannan sashe.
A don haka ta yi kiran da a bullo da manyan ayyukan da za su kara bunkasa wannan bangare a nahiyar, kamar gina madatsun ruwa.
Wakilai 650 daga kasashe 66 sun halarci wannan taro na yini uku mai taken "matakan adana ruwa da samar da wutan lantarki bisa karfin ruwa a Afirka". (Ibrahim Yaya)