Mataimakin kwamishinan gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU Thomas Kwesi Quartey, ya bayyana cewa, samar da hadin kai wajen aiwatar da muhimman shirye-shiryen kungiyar ta AU mataki ne da zai haifar da gagarumin cigaba.
Quartey, ya shedawa 'yan jaridu a wajen taron kolin AU karo 29 a Addis Ababa na kasar Habasha cewa, idan aka samu nasarar aiwatar da sauye sauyen, zai taimakawa kasashen Afrika wajen shawo kan kalubalolin dake neman zama tarnaki wajen aiwatar da manufofin AU na cigaba.
A cewarsa hanyoyin samun kudade wani muhimmin bangare ne dake bukatar a yi masa kwaskwarima, domin baiwa kungiyar ta AU 'yancin cin gashin kanta ta fuskar gudanar da sha'anin kudi.
Dama dai shugabannin kasashen mambobin kungiyar ta AU sun rattaba hannu kan batun sauya fasalin kudi na kungiyar a lokacin taron kolin kungiyar karo na 27 da aka gudanar a kasar Ruwanda a bara.(Ahmad Fagam)