Masu tayar da kayar baya dake yin biyayya ga huhumomin gabashi sun sanar a ranar Asabar cewa sun saki Saif Gaddafi ne a ranar Juma'a, kuma ya bar yankin Zintan tun tuni. Amma ba'a san takamamman inda yake ba a halin yanzu.
Sai dai kawo yanzu, gwamnatin Libyan ba ta ce uffan ba game da batun sakin nasa.
Ana tsare da Saif Gaddafi ne tun a shekarar 2011 a Zintan, garin ne dake yankin kudu maso yammacin babban birnin kasar Tripoli. Ana zarginsa ne da haddasa tashin hankali da kuma hallaka masu zanga zanga a lokacin tarzomar da ta barke a kasar a shekarar 2011 wadda ta yi sanadiyyar tunbuke mahaifinsa daga karagar mulkin kasar.
Wata kotu a Tripoli ta zartar da hukuncin kisa kan Saif Gaddafi, wanda a baya ake gani a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa, an yanke masa hukuncin kisan ne tare da wasu tsaffin jami'an tsohuwar gwamnatin Libyan a shekarar 2015.
Sai dai kuma, majalsiar dake zamanta a gabashi, ta yi wa Saif Al-Islam din afuwa jim kadan bayan yanke masa hukuncin.
Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa ICC ita ma take neman Saif Gaddafi ruwa a jallo, bisa zarginsa da aikata cin zarafin bil adama a lokacin tarzomar kasar a 2011. Sai dai kuma mayakan sun ki amincewa su mika shi ga kotun ta ICC.