Cikin wani sakon faifan bidiyo da Shugaba Xi ya aikewa rundunar soji ta kasa da kasa wanda kasar Rasha ta kafa inda ta gudanar da gasanninta na shekarar 2017, Xi ya ce hadin gwiwar sojojin kasa da kasa zai kara tabbatar da amincewa tsakanin dakarun, kana zai tabbatar da zaman lafiya a matakan shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.
Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar tsakiya mai kula da sojoji wato CMC, ya aike da sakonsa na fatan alheri a madadin gwamnatin kasar Sin cikin faifan bidiyo.
An shirya gasar sojojin ne ta shekarar 2017, wanda za'a gudanar a ranar 12 ga watan Augusta, bikin ya kunshi wasanni 28 wanda ya hada da kasashen Rasha, Sin, Azerbaijan, Belarus da Kazakhstan. (Ahmad Fagam)