in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi amfani da sabon jirgin yaki na ruwa kirar kasar Sin domin wanzar da zaman lafiya a duniya
2017-06-30 09:06:15 cri

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya ce sabon jirgin ruwan yaki kirar kasar Sin mai suna "China new destroyer" zai taimaka, wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaito a duniya.

Wu Qian, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya ce manufofin tsaro na kasar Sin a bayyane su ke kuma ba za su sauya ba, duba da cewa sun maida hankali ne kadai ga bunkasa tsaron kasar Sin ta fuskar samar da kayayyakin aiki na zamani, tare da gina rundunar soji mai cike da kwararrun dakaru.

Sabon jirgin ruwan yakin dai na da nauyin tan 10,000 yana kuma dauke da kayan tsaron sararin samaniya, da na'urorin kakkabo makamai masu linzami, da na dakile hare haren jiragen ruwa ko jirage masu nutso a karkashin ruwa.

An dai kaddamar da wannan jirgin ruwa na yaki ne a ranar Laraba, a tashar jirgin ruwan Jiangnan dake birnin Shanghai.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China