in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara atisayen sojan ruwa a tsakanin Sin da Rasha
2017-07-23 13:39:39 cri

A jiya Asabar aka fara atisayen sojan ruwa na shekarar 2017 a tsakanin Sin da Rasha a tashar jiragen ruwa ta Baltiysk da ke kasar ta Rasha.

Mr. Tian Zhong, babban darektan atisayen daga bangaren Sin, wanda kuma shi ne mataimakin babban kwamandan rundunar sojan ruwa ta kasar Sin ya ce, jerin atisayen sojan ruwa da kasashen Sin da Rasha suka gudanar cikin hadin gwiwa, mataki ne na daukaka huldar hadin gwiwa da abokantaka a tsakanin kasashen biyu, haka kuma muhimmin mataki ne na inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin sojojin kasashen biyu, musamman ma sojan ruwa, wanda ka iya taimakawa ga kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da kuma shiyyar. A bana, sojojin kasashen biyu za su maida hankali a kan barazanar ta'addanci da ake fuskanta a yayin gudanar da harkokin tattalin arziki a teku da kuma samar da agajin gaggawa, don kara daukaka hadin gwiwarsu.

A nasa bangaren, Mr. Aleksandr Fedotenkov, babban darektan atisayen daga bangaren Rasha, kuma mataimakin babban kwamandan rundunar sojan ruwa ta kasar Rasha, ya ce, tun bayan da aka fara aiwatar da atisayen sojan ruwa a tsakanin kasashen biyu a shekarar 2012, an yi ta ingantawa da kuma daukaka matsayin atisayen. Babu shakka, atisayen sojan ruwa da aka gudanar a wannan karo, zai sa kaimin hadin gwiwa a tsakanin sojojin ruwa na kasashen biyu, tare kuma da karfafa dankon zumunci a tsakaninsu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China