in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 3 sun mutu a sakamakon harin da aka kai wani kauye dake arewacin kasar Burkina Faso
2017-07-29 13:59:24 cri
Rahotanni daga kafofin watsa labaru na kasar Burkina Faso sun ce, harin da wasu bata gari suka kai kan wani kauyen jihar Soum dake arewacin kasar, ya haddasa mutuwar mutane a kalla 3.

Rahotannin da aka fitar a jiya, sun bayyana cewa, a daren ranar 27 ga wata, wasu bata gari sun kai hari ba zato ba tsammani kan wani kauye dake jihar Soum, wanda ya haddasa mutuwar wani dan majalisar dokokin birnin da iyalansa guda biyu, sannan suka kwace dabbobin da dama da mazauna kauyen ke kiwo.

Zuwa yanzu, Gwamnatin kasar Burkina Faso ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba, haka zalika babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakinsa.

Tun daga daren ranar 24 zuwa safiyar ranar 25 ga wata, wasu tsageru sun kai hare-hare kan kauyuka 3 na jihar Soum, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 5.

Hukumar kiyaye tsaro ta kasar ta bayar da labarin cewa, mutanen 5 membobi ne na wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi. Kuma an yi zaton cewa, kungiyar ce ta kai hare-haren domin hukunta su. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China