Da yake jawabi jiya, yayin bude taron kasa da kasa kan bunkasa nahiyar Afrika a birnin Casablanca na kasar Morocco, Christian Kabore ya yi kira da kasashen Afika su hada hannu wajen tunkarar kalubalen da nahiyar ke fuskanta a dukkan bangarori, yana mai jadadda cewa, kamata ya yi manufofin tattalin arzikin yankin su mai da hankali ga masu karamin karfi da gajiyayyu.
Ya ce dole ne shugabnnin nahiyar da 'yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki su dauki managartan matakai da za su taimaka wajen tabbatar da habakar tattalin arziki da kuma inganta walwalar al'umma ta yadda za a samu dawwamammen zaman lafiya a Afrika da ma duniya baki daya.
Taron na yini biyu mai taken 'sabbin manufofin ci gaba da ya kunshi dukkan bangarori a Afrika' ya samu mahalarta 1,500 daga kasashen nahiyar 25 da kuma wasu kasashe. (Fa'iza Mustapha)