Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce kalubalen tsaro da ake fuskanta a yanzu, ya jefa harkokin yada labarai cikin mawuyacin hali, abun da ke tarnaki ga aikin jarida.
Za a yi amfani da Shirin mai taken 'kafafen watsa labarai da tsaro' ne a lokacin da aka samu barkewar ayyukan ta'addanci a kasar, musammam ma a yankin arewacin kasar dake iyaka da kasashen Mali da Niger.
Cikin 'yan shekarun da suka gabata, kasar Burkina Faso ta yi fama da hare-haren ta'addanci, inda wasu alkaluma a hukumance ke cewa hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane sama da 70 cikin shekarar 2015. (Fa'iza Mustapha)