Wata sanarwa da Gwamnatin ta fitar jiya, ta ruwaito matakan sun hada da kaddamar da cibiyoyin tura ruwa guda 47 da kuma samar da ruwa ta wata hanya ta daban duk bayan sa'o'i 12 ga wasu yankunan birnin Ouagadougou dake fuskantar matsalar,.
Baya ga wannan, hukumomin kasar na shirin haka karin rijiyoyi 36 masu fanfon tuka-tuka ko kuma wadanda ke amfani da hasken rana. (Fa'iza Mustapha)