A lokacin da yake hira da manema labarai a yayin taron ayyukan ciniki na kasar Sin, mista Tang Wenhong ya bayyana cewa, babu canji kan yanayin zuba jari a nan kasar Sin da kwarewar kasar ta bangaren jawo jari, kuma kasar Sin ta fi kwarewa a fannonin tsarin dokoki, yanayin ciniki, kwadago da dai sauransu.
Ban da wannan kuma, Tang Wenhong ya ce, don kara jawo jari daga kasashen waje, kasar Sin tana kokarin kyautata yanayin zuba jari a dukkan fannoni, da samar da yanayin yin ciniki bisa adalci a bayyane domin jama'a. Kana ya kiyasta cewa, Sin za ta kiyaye jawo jari daga kasashen waje a shekarar 2015, da yawan jarin da za ta jawo zai yi daidai da na shekarar 2014. (Zainab)