in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan jarin waje da Sin ta yi amfani da shi a farkon watanni 3 na bana ya karu da kashi 4.5 cikin dari
2016-04-13 11:03:34 cri

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, a farkon watanni 3 na shekarar bana, yawan jarin waje da Sin ta yi amfani da shi ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 224.21, wanda ya karu da kashi 4.5 cikin dari bisa makamancin lokacin bara.

Alkaluman da ma'aikatar ta samar sun nuna cewa, a wadannan watanni 3, kasar Sin ta kara samun kamfannoni masu jarin waje 5956, wanda ya karu da kashi 1.6 cikin dari bisa makamancin lokacin bara.

Bugu da kari, sana'ar ba da hidima ta fasaha ta fi samun yawan jerin waje. Alkaluman sun bayyana cewa, yawan jarin waje da wadannan kamfannoni suka yi amfani da su ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 154.38, wanda ya karu da kashi 7.6 cikin dari bisa makamancin lokacin bara.

A galibi dai, manyan kasashen da suka fi zuba jari a kasar Sin sun ci gaba da kiyaye matsayinsu a wannan fanni, kana kasashen da shirin "ziri daya da hanya daya" ya shafa sun kara yawan jarin da suka zuba a kasar Sin, wadanda suka kafa kamfanoni 558 a kasar Sin, jimlara da ta karu da kashi 21.6 cikin dari bisa makamancin lokacin bara, sa'an nan, yawan kudin da suka zuba ya kai dalar Amurka biliyan 1.84, wanda ya karu da kashi 8 cikin dari.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China