in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya zata kwace shaidar izinin dan kasa na 'yan gudun hijira dake karya doka
2016-08-22 10:20:56 cri
Firaiministan kasar Tanzaniya Kassim Majaliwa ya fada cewar, gwamnatin kasar a shirye take ta kwace takardun izinin dan kasar na 'yan gudun hijirar Burundi wadanda basa mutunta doka.

Majaliwa, ya fadawa 'yan gudun hijirar Burundi da aka baiwa shedar zama 'yan kasa dake zaune a garin Katumba a lardin Katavi na kasar Tanzaniya cewa, gwamnatin zata janye izinin zama 'yan kasar ga 'yan asalin kasar Burundin dake gudun hijira a kasar wadanda basa yin biyayya. Kuma za'a mayar dasu zuwa kasashen su na asali.

Firaministan wanda ke ziyarar aiki a yankin, ya jaddada cewa akwai yiwuwar 'yan gudun hijirar zasu fuskanci fushin gwamnati sakamakon karya doka da suke yi, ta hanyar debo wasu 'yan uwansu zuwa kasar. Ya ce sam gwamnatin ba zata amince da aikata hakan ba.

Majaliwa, ya umarci kwamitin jami'an tsaro dake lura da yankin na Katavi dasu gudanar da bincike na musamman a sansanin 'yan gudun hijira na Katumba da Mishamo domin gano ko akwai 'yan gudun hijirar masu shaidar dan kasa da suka kwaso 'yan uwansu zuwa yankin.

Yace binciken zai shafi batun gano ko akwai 'yan gudun hijirar da suka mallaki makamai ba bisa ka'ida ba.

Majaliwa yace, 'yan sandan kasar Tanzaniya ne kadai doka ta basu damar rike makamai.

Ya kara da cewar za'a tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar domin hana 'yan gudun hijirar sulalewa zuwa kasashen gabashin Afrika ta haramtattun hanyoyi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China