in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 11 sun mutu wasu 200 sun jikkata sanadiyyar girgizar kasa a Tanzaniya
2016-09-11 12:58:47 cri
'Yan sanda a Tanzaniya sun ce, a kalla mutane 11 aka tabbatar da mutuwarsu, sannan sama da mutane 200 suka samu raunuka a sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 5 da digo 7 data afkawa yankin arewa maso yammacin kasar a jiya Asabar.

Girgizar kasar ta afku ne a lardin Kagera da Mwanza dake shiyyar arewa maso yammacin kasar ta Tanzaniya.

Kwamandan hukumar 'yan sandan yankin Kagera Augustino Olomi ya ce a kalla mutane 11 sun hallaka, sannan sama da mutane 200 kuma sun samu raunuka a sakamakon girgizar kasar.

Salum Kijuu, kwamishinan shiyyar Kagera ya shedawa kamfanin dillancin labaran Xinhua ta wayar hannu cewa, girgizar kasar ta yi sanadiyyar daruruwan mutane sun rasa matsugunansu da kuma hasarar dukiyoyi.

Ya kara da cewa, har yanzu ba za'a iya tantance hakikanin alkaluma na mutanen da suka jikkata ba, da kuma irin hasarar dukiyoyi da gidajen da aka samu ba, sai dai a cewarsa, an tura jami'an aikin ceto zuwa yankunan da lamarin ya afku.

Kijuu yace, tuni aka garzaya da wadansa suka samu raunuka zuwa asibiti domin basu kulawa.

A cewarsa lamarin ya faru ne da misalign karfe 9 da rabi na safiyar ranar Asabar, lamarin da ya jefa mutane cikin damuwa suka bar dukiyoyinsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China