Shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya yi wa majalisar dokokin kasar bayanin halin da ake ciki a kasar dangane da harkokin tsaro da na kudi da kuma dangantaka da kasashen waje wadda aka yi wasarairai da ita cikin gomman shekaru.
Da yake bayanin a jiya, Adama Barrow ya ce, gwamnati na aiki kan sake fasalin bangaren tsaro wanda ya ce na da alaka ta kut-da-kut da tabbatar da adalci tare da sahihin tsarin demokradiyya.
Shugaban ya kuma yaba wa kungiyar ECOWAS ta raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, da ta ba da dakarunta na ECOMIG don kare kasar. (Fa'iza Mustapha)