Shugaban tawagar kungiyar ta AU da aka tura kasar ta Gambia Pierre Buyoyo shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wata ganawar sirri da tawagar ta yi da mataimakiyar shugaban kasar Fatoumatta Jallow Tambajang.
Ya ce ziyarar tawagar ta mai da hankali ne kan yadda za a taimakawa kasar Gambia ta gudanar da sauye-sauye a fannin tsaro, tattalin arziki da kuma yadda za a kafa hukumar tsage gaskiya da sasantawa ta kasar(TRC)