in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambiya ta sake nanata matsayinta na goyon-bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya
2017-02-25 13:09:00 cri
Jiya Jumma'a ne, ma'aikatar harkokin wajen kasar Gambiya ta fitar da wata sanarwa, inda ta jaddada cewa, gwamnatin kasar ta tsaya haikan kan manufar kasar Sin daya tak a fadin duniya, kuma gwamnatin Jamhumriyar Jama'ar kasar Sin, halastacciyar gwamnati ce daya tilo dake wakiltar kasar Sin a duniya, yayin da Taiwan ya kasance wani yanki da ba za'a iya balle shi daga kasar Sin ba.

Sanarwar ta sake nanata cewa, gwamnatin kasar Gambiya na mutunta cikakken yankin kasar Sin, kuma ta yi alkawarin cewa, ba za ta kulla duk wata dangantaka da Taiwan ba, haka kuma ba za ta yi mu'amala da ita a hukumance ba.

A ranar 17 ga watan Maris din bara ne a birnin Beijing, ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Gambiya, wato Mista Wang Yi da Madam Neneh MacDouall-Gaye suka rattaba hannu kan wata hadaddiyar sanarwa, dangane da farfado da dangantakar jakadanci tsakanin Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin da Jamhuriyar Gambiya, kuma tun daga wancan lokaci ne suka dawo da dangantakar diflomasiyya dake tsakaninsu.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China