in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Gambia zai fara rangadi a kasashe 4 na mambobin kungiyar ECOWAS
2017-04-26 09:35:18 cri
Ministan yada labarai na kasar Gambia Demba Jawo, ya sanar da cewa, Shugaban kasar Adama Barrow, zai fara rangadi a kasashe mambobin ECOWAS da suka tsaya masa lokacin rikicin siyasar kasar.

Demba Jawo ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Talata cewa, Shugaban kasar zai fara rangadin ne a yau Laraba, inda zai ziyarci kasashe da suka hada da Ghana da Saliyo da Najeriya da kuma Liberia.

Shugaba Adama Barrow, ya kama aiki ne bayan rikicin zabe da aka yi a shekarar da ta gabata, zaben da shugabannin kasashen ECOWAS suka bayyana a matsayin sahihi mai cike da adalci.

Magabacinsa Yahaya Jammeh, ya yi rashin nasara a zaben na 1 ga watan Decembar bara, inda kuma ya amince da sakamakon, sai dai kuma, mako guda bayan nan, ya janye furucin nasa, yana mai ikirarin cewa, zaben na kunshe da kura-kurai. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China