in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambia na shirin kafa hukumar tsare gaskiya da warware rikici cikin watannin shida
2017-03-24 12:30:53 cri
Ministan Shari'a na kasar Gambia Abubacarr Tambadou ya sanar da cewa, gwamnatin kasar za ta kafa wata hukumar tsare gaskiya da warware rikice-rikice cikin watanni shida masu zuwa, wadda za ta yi bincike kan laifukan da ake zargin tsoffin jami'an gwamnatin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh da aikatawa.

Abubakar Tambadou ya ce za a kafa hukumar ne tare da shirya diyya ga wandanda aka zalunta cikin watanni shida. Sannan, ana sa ran sauraron ra'ayoyin jama'a a karshen shekara.

Da yake jawabi jiya, yayin wani taron manema labarai, Ministan ya ce hukumar za ta yi amfani da wasu matakai da hukumomi takwarorinta suka yi amfani da su.

Ya kara da cewa, zai kuma yi kira da a cire hukuncin kisa daga cikin kundin tsarin mulkin kasar da za a yi wa gyaran fuska.

A halin yanzu shugaban hukumar leken asiri na tsohon shugaba Jammeh da wasu manyan jami'an hukumar, na fuskantar shari'a a kotu kan laifuka da dama da suka hada da shirya kisan al'ummar kasar da dama, ciki har da wani mai rajin kare tsarin siyaysa Ebria Solo Sandeng da ma al'ummar kasashen waje. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China