in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya tallafawa Gambia da dala miliyan 56
2017-07-12 14:59:37 cri
Babban bankin duniya ya tallafawa kasar Gambia da kudi har dala miliyan 56, a matsayin taimakon farfadowa, da samar da ababen more rayuwa da al'ummar kasar ke matukar bukata.

Da take tabbatar da hakan, babbar daraktar bankin a kasar Gambia Lousie Cord, ta ce hakan wani bangare ne alkawarin da bankin ya dauka tun da fari, na agazawa kasar wajen cimma nasarar mika mulki ga gwamnatin da 'yan kasar za su amince da ita.

Lousie Cord, ta ce bankin duniya ya tanaji tallafi kashi biyu ga kasar ta Gambia, wanda ya hada da kashin farko mai kunshe da kaso 55 bisa dari na bashi da za a biya cikin shekaru 40, yayin da kuma ragowar kaso 45 zai zamo kyauta ga kasar.

A nasa tsokacin, ministan kudi da raya tattakin arzikin kasar Gambia Amadou Sanneh, ya ce tsarin ci gaban tattalin arzikin kasar na bara, ya yi matukar tasiri idan aka kwatanta da na shekarun da suka shude, lokacin da kasar ke fuskantar rub-da-ciki kan dukiyar al'umma, da ma takunkumi da aka rika kakabawa kasar.

Mr. Sanneh, ya ce ci gaban tattalin arzikin Gambia a shekarar bara ya karu da kaso 2.2 cikin dari, kasa da kaso 4.3 bisa dari da kasar ta samu a shekarar 2015. Ya ce hakan ya faru ne sakamakon karancin kudaden musayar kasashen ketare, da kamfar amfanin gona da aka sha fama da ita, tare da matsalar siyasa da ta dakile harkokin yawon shakatawa a kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China