in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farashin kayayyakin da ake sarrafawa a kasar Sin ya tashi da kashi 5.5 a watan Yuni
2017-07-10 13:56:31 cri
Alkaluman farashin kayayyakin da ake sarrafawa wato PPI a kasar Sin ya karu da kashi 5.5 cikin dari a watan Yuni bisa na makamancin lokacin na bara, ko da yake alkaluman bai sauya ba a watan Mayun bana.

An bayyana alkaluman ne tare da na awon farashin kayayakin masarufi wanda ya tashi da kaso 1.5 cikin dari a watan Yunin bisa na makamancin lokacin bara, ba tare da wani sauyi ba bisa na watan Mayun bana.

Hukumar kiddiga ta kasar Sin ta alakanta raguwar alkaluman da raguwar farashin abinci, wanda ya sauka da kashi 1 tun daga watannin baya zuwa watan Yuni. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China