in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 6.9 a tsakiyar shekarar 2017
2017-07-17 11:06:10 cri

Tattalin arzikin GDP na kasar Sin ya karu da kashi 6.9 bisa 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a shekarar bara da kusan yuan triliyan 38.15 kwatankwacin dalar Amurk triliyan 5.62, hukumar kididdigar ta kasar Sin ce ta tabbatar da hakan a yau Litinin.

GDP na kasar ya karu ne da kashi 6.9 bisa 100 tun watanni ukun farko na wannan shekara ta 2017, kamar yadda hukumar kididdigar ta kasar Sin ce ta tabbatar .

Kayayyakin da masana'antun kasar Sin ke fitarwa, ya kasance wani muhimmin alamu na karuwar tattalin arzikin kasar, inda a tsakiyar wannan shekarar ta bana ya karu da kashi 6.9 sama da watanni ukun farko na wannan shekara inda ya karu da kashi 6.8 bisa 100. Cinikin kayayyakin bukatun yau da kullum ya karu da kashi 10.4 bisa 100 a tsakiyar shekarar 2017 idan aka kwatanta da makamancin lokaci a shekarar da ta gabata.

Haka zalika a fannin hada hadar hannayen jari ma, a watanni shida na wannan shekara ya karu daga kashi 8.5 bisa 100 zuwa kashi 8.8 bisa 100 tsakanin watanni Janairu zuwa Yunin wannann shekara kamar yadda hukumar kidddigar ta kasar Sin ta sanar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China