in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CPPCC ya gana da mataimakin shugaban Ghana
2017-06-23 20:51:24 cri

A yau Jumma'a ne shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin wato CPPCC Mr. Yu Zhengsheng, ya gana da mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia a nan Beijing.

A yayin ganawar tasu mista Yu ya ce, kasar Sin na fatan ci gaba da hada kai da Ghana, wajen kara azama ga hadin gwiwar abokantaka a tsakaninsu, a kokarin kara sada daukacin al'ummun kasashen biyu da alherai.

Shi kuwa a nasa bangare mista Bawumia ya ce, kasarsa na da burin koyi daga fasahohin kasar Sin a fannin raya kasa, da shiga ayyuka da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa, da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin a fannoni daban daban, a wani mataki na daga matsayin huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China