in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya Rouhani murnar sake lashen zaben shugabancin Iran
2017-05-21 13:24:29 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga takwaransa shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, saboda sake lashe zabarsa da aka yi a matsayin shugabancin kasar na wa'adin shekaru 4 a karo na biyu.

Cikin sakon da ya aike shugaba Xi, ya bayyana cewa a wa'adin mulkin Rouhani na shekaru hudun farko, ya samu gagarumar nasarar raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Iran, kana ya bayyana cewar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Iran ta kara samun cigaba zuwa wani babban mataki sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Idan za'a iya tunawa, a watan Janairun shekarar 2016 ne shugaban kasar Sin ya ziyarci Tehran, inda shugabannin kasashen biyu suka yi tattaunawa mai zurfi, a yayin tatttaunawar Xi ya bayyana cewa sun cimma matsaya guda game da wasu muhimman batutuwan diplomasiyya, wadanda za su kara ingiza kyakkyawan hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kara da cewa yana daukar batun dangantaka dake tsakanin kasashen biyu da muhimmanci, kuma a shirye yake ya hada gwiwa da Rouhani wajen kara karfafa kyakkyawar mu'ammala dake tsakanin Sin da Iran.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China