Wannan kira dai na zuwa ne, bayan da Amurka ta kakabawa wasu sassa da daidaikun mutane 18 karin takunkumi a ranar Talata. An ce sassan da takunkumin ya shafa dai na da alaka ne da ayyukan kasar da suka shafi sarrafa makamai masu linzami, da wasu makaman wadanda ba na nukiliya ba.
A hannu guda Sin ta bayyana rashin goyon bayan ta, ga duk wasu matakai na yaduwar makaman nukiliya a duniya, ko fakewa da wata dama domin habaka sashen bisa dogaro da dokokin cikin gida.