Mr Wu wanda ya bayyana hakan a jiya yayin wani taro da kwamitin sulhun MDD ya shirya game da batun nukiliyar Iran, ya bayyana cewa, an aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran yadda ya kamata a cikin shekarar da ta gabata, amma duk da haka, akwai matsala da kuma kalubale, wadanda ke bukatar hada kai daga bangarori daban daban.
Wu Haitao ya ce, kullum kasar Sin tana nacewa ga warware batun nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya da inganta tsarin hana yaduwar makaman nukiliya da kiyaye zaman lafiya a duniya.(Lubabatu)