in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi bayani game da hadin gwiwar yaki da talauci da samun bunkasuwa a tsakanin Sin da Afirka
2017-06-22 11:14:25 cri
A jiya ranar 21 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki sun gana da 'yan jarida tare, inda Wang Yi ya yi bayani game da hadin gwiwar yaki da talauci da samun bunkasuwa a tsakanin Sin da Afirka.

Wang Yi ya bayyana cewa, talauci shi ne abokin gaba na dan Adam, kana shi ne tushe na samun yawaitar tashe-tashen hankula da ta'addanci. Bunkasuwa hanya ce mafi muhimmanci wajen warware dukkan matsaloli, kana ita ce burin da Sin da Afirka da kasashe masu tasowa suke son cimmawa.

Sin da Afirka su ne abokai wajen yaki da talauci da samun bunkasuwa. Bisa bukatun Afirka tare da fasahohin Sin, Sin za ta kara yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka a fannoni 5 don yaki da talauci, wato kara nuna imani kan fita da kangin talauci, da koyar da fasahohi, da ba da taimakon gaggawa, da gina hanyoyin sufuri, da kuma kyautata tsarin kiwon lafiyar jama'ar Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China