in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Habasha ya gana da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi
2017-06-22 10:31:34 cri
A jiya ne, firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi dake ziyara a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Wang Yi ya bayyana cewa, bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, an samu bunkasuwa cikin sauri a fannin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Habasha, a muhimman matakai uku, na farko kasar Habasha tana daya daga cikin kasashe na farko a Afirka da suka yi hadin gwiwar samar da kayayyaki da Sin. Na biyu Habasha ta zama muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa a fannin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", na uku Habasha ta kasance abokiyar hadin gwiwar kasar Sin bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a halin yanzu.

A nasa bangare, Hailemariam ya bayyana cewa, kasarsa wato Habasha tana son yin amfani da damar "ziri daya da hanya daya", don kyautata tsarin tattalin arzikin kasar. Kasar Habasha tana farin ciki da zama abokiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni ta kasar Sin, kuma wannan zai taimaka wajen kara raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China