170720-Federer-ya-lashe-kofin-Wimbledon-karo-na-8-zainab.m4a
|
Masu sharhi dai na cewa, Cilic na fama da ciwo a kafar sa ta hagu lokacin da suka buga wasan na karshe. Ya kuma yi iya kokarin lashe wasan, kafin Federer ya samu galaba a kan sa a zagaye na 7 na wasan.
Rabon Federer da daukar wannan kofi dai tun a shekarar 2012, da kuma wannan nasara yawan manyan gasannin da ya lashe suka kai 19. Tuni dai dan wasan ya nuna matukar farin ciki da wannan nasara da ya samu, yana mai cewa, ya yi farin cikin ganin manyan baki da suka kasance tare da shi a wannan wasa mai matukar tarihi. Ya kuma yi fatan badi ma zai dawo domin ya kare kanbun na sa.
Federer wanda dan kasar Switzerland ne, kuma shi ne dan wasa ma fi shekaru da ya lashe gasar Wimbledon, tun bayan da aka sauya mata suna zuwa Open. Yanzu haka dai a jerin 'yan wasa mafiya kwarewa a kwallon Tenis Federer mai shekaru 35 shi ne na 3, wanda hakan ke nuna mafificiyar daukaka da ya samu, tun cikin watan Agustar shekarar 2016. (Saminu Alhassan)