Hukumar ta ce janyewar 'yan wasan ya sabawa dokoki da da'ar wasanni da aka saba da ita.
'Yan wasan dai Ma Long, da Xu Xin, da Fan Zhendong tare da masu horas da su; koci Qin Zhijian, da Ma Lin, sun yi watsi da zagaye na 2 da ya dace su buga na gasar ajin maza. An dai tsara buga wasannin ne da misalin karfe 8 saura minti 20 na daren ranar Juma'ar da ta gabata, a birnin Chengdu fadar mulkin lardin Sichuan.
Kafin hakan, an ce 'yan wasan da masu horas da su 2, sun sanar ta shafukan su na sada zumunta da misalin karfe 7 na daren ranar suna masu cewa, ba za su halarci wasan da ya dace su buga ba, saboda kewar malam Liu Guoliang, wanda shi ne babban mai horas da 'yan wasan kwallon Tennis na kasar Sin.
Kwanaki 3 kafin hakan ne aka nada Liu a matsayin mataimakin shugaban hukumar Tennis na kasar Sin, aka kuma cire shi daga tsohon mukamin sa na horaswa.
An ce sauyin matsayin da aka yiwa Liu, ya biyo bayan wani gyaran fuska ne da aka yiwa harkar gudanar da wasan na Tennis a kasar baki daya. Bisa sabon tsarin an rushe matsayin babban mai horas da 'yan wasa daga tawagar kasar, maimakon sa kuma an kirkiri tsarin tawagogin horas da 'yan wasa biyu biyu, ga ajin maza da na mata masu wakiltar kasar.
Hukumar wasannin kasar, ta ce sauyin zai bada karin dama ta horas da 'yan wasan da za su wakilci kasar Sin a gasar Olympic ta shekarar 2020 wadda za a gudanar a birnin Tokyon kasar Japan.(Saminu Alhassan)