in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Djokovic ya lashe kofi a gasar wasan tennis ta China Open
2015-10-15 09:31:21 cri

Novak Djokovic ya yi nasara a kan abokin karawarsa Rafael Nadal a duk zagaye 2 na wasan karshe da ya gudana tsakaninsu a babbar gasar wasan tennis ta China Open a ranar Lahadi, don haka yanzu Djokovic ya samu kofinsa na 6 a gasar China Open, nasarar da ya samu a karon farko, ta sa abokin karawar tasa Nadal ya sha kaye, wanda a baya bai taba shan kaye ba a duk wata gasar da ya halarta.

A wasan da ya gudana ranar Lahadi, Djokovic, dan kasar Serbia, ya lashe Nadal da ci 6 da 2 a zagayen farko, sannan ci 6 da 2 a zagaye na 2. Duk da cewa Nadal din ya kasance fitaccen dan wasan wanda ya taba zama zakara a manyan gasar wasannin tennis 14, to amma a wannan kakar wasan da muke ciki, yana fada cikin wani yanayi maras kyau, bisa la'akari da yadda ya kasa samun kofi ko guda a shekarar da ta gabata.

A nashi bangare, Djokovic ya riga ya samu kofuna 8 a kakar wasan da muke ciki, ciki har da kofuna 3 na manyan gasar wasanni 4 masu matukar muhimmanci a fannin wasan tennis wato Grand Slam a Turance.

A halin yanzu, Djokovic na bukatar wasa samun nasara a wasa daya ne kacal zai iya yin kunnen doki da Nadal bisa sakamakon da aka samu a wasannin da ya gudana a tsakaninsu, ganin yadda 'yan wasan suka taba karawa da juna a wasanni 45, yayin da Nadal ya ci nasara a wasanni 23 daga cikinsu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China