Shahararren dan wasan fina-finai na kasar Amurka Bill Murray ne ya jagoranci bikin gabatar da kyautar, yayin da sauran mahalarta bikin suka hada da shahararrun 'yan wasan kasashe daban daban, masu ritaya gami da wadanda tauraronsu ke haskaka a yanzu. An kaddamar da bikin ne don girmama fitattun 'yan wasa maza da 'yan mata, wadanda suka fi taka rawar gani a shekarar da ta gabata.
A nasa bangare, shahararren dan wasan kwallon tennis Novak Djokovic, wanda ya lashe kambin manyan gasannin wasan kwallon tennis na Grand Slam har karo 3, ya samu zama fitaccen dan wasan na shekara a bikin gabatar da kyautar Laureus karo 2 a jere, kuma hakan ya kasance karo na 3 da ya samu wannan babbar lambar yabo.
Yayin da Serena Williams, 'yar wasa daga Amurka, ta samu kyautar Laureus ta 4, bayan da ta ci nasarori da yawa a shekarar 2015 da ta wuce, inda ta kusan lashe dukkannin kofunan zinariya a manyan gasannin wasan kwallon tennis na Grand Slam da suka gudana a shekarar.(Bello Wang)