Membobi 83 sun halarci cikakken zama a wannan karo, inda suka amince da zartas da kudurin da kwamitin gudanarwa na hukumar IOC ya gabatar a watan da ya gabata, wato yadda daya daga cikin birane biyu da suke neman daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024 zai cimma nasarar samun izinin, yayin da dayan zai samu iznin daukar bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics ta shekarar 2028. Da wannan mataki za a cimma dacewa da moriyar wasannin Olympics a dogon lokaci.
Ana dai daukar wannan sakamako a matsayin nasarar da shugaban hukumar IOC Thomas Bach ya samu, domin membobin hukumar sun ki amincewa da shawarar da ya gabatar karon farko da ya bayyana ta a farkon shekarar bana. (Zainab)