170525-Zidane-yana-farin-ciki-da-samun-nasara-a-gasar-league-zainab.m4a
|
Kwallayen da Cristiano Ronaldo da Karim Benzema suka zarawa Madrid shine ya basu dama kan Malaga.
"Muna matukar farin ciki inji Zidane bayan wasan. Bayan makonni 38, mun zo nan kuma mun yi galaba a wasannin na duniya."
"Babu wani abu da yafi kyau a matsayin zama kwararren koci wannan shine abu mafi dadi a rayuwatae," inji shugaban kungiyar kwallon kafan ta Madrid, wanda ya yabawa tawagar yan wasan nasa.
"Yan wasan sun cancanci wannan yabo koda yake dukkanmu mun sha wuya, sune wadanda suka sha gudu kuma suka wahala. Dukkansu suna da muhimmanci kuma dunkulewar kungiyar yan wasan waje guda shine jigon da ya bamu nasara."
Real Madrid zata kara da Juventus a wasan karshe na Champions League a ranar 3 ga wata Yuni, amma a karshe an ga yadda Barcelona ta lashe matsayi na 3 da Atletico Madrid a gaba, muhimmin abu ne ga Zidane.
" wasan shine aikin na yau da kullum kuma yana da muhimmanci idan kayi nasara koda a Madrid ne," inji Zidane. (Ahmad Fagam)