Deusdedit Kakoko, darekta janar na TPA, ya bayyana cewa sabon tsarin da ake kira tsayin yin amfani da tashar ruwa (POS), zai taimakawa TPA, tsakanin ba da labari kai tsaye tare da masu shigo da kayayyaki da masu aikawa da kayayyaki ta yadda za a rage dama ga ma'aikatan share fage da na aike nuna ha'inci wajen zaluntar dan kasuwa ba tare da shakku ba.
Haha kuma ya kara da cewa, tare da wannan sabon tsarin, ba za a sami wata dama ga wani ma'aikacin share fage da aikawa na ya yi yaudara bisa kagon kayayyaki ba.
Mista Kakoko ya nuna cewa TPA ya tsaida shirin zuba dalar Amurka miliyan 690 a matsayin wani rancen kyautata da zuba jari na bankin duniya, da Trade Mark East Afrika da kuma Cibiyar Burtaniya kan bunkasuwar kasa da kasa (DFID), da za a yi amfani da shi domin aiwatar da a kalla manyan ayyukan tashoshin ruwa guda goma sha uku. (Maman Ada)