A cewar hukumar, kasar za ta yi amfani da karin iskar gas a bangaroin da suka hada da na samar da lantarki daga iskar gas da sufuri kuma masana'antu.
Yawan amfani da iskar gas zai kai kusan kashi 10 cikin dari na makamashin da ake amfani da shi a kasar kawo shekarar 2020.
Kasar Sin na shirin rage yawan iskar dake gurbata muhalli da take fitarwa ya zuwa shekarar 2030, da kashi 60 zuwa 65 cikin dari na nau'in GDP, daga matakin da take kai a shekarar 2005. (Fa'iza Mustapha)