Wani babban jami'i a asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya bayyana cewa, kasar Sin tana da dukkan abubuwan da za su ci gaba da rike bunkasar da ta samu cikin matsakaicin lokaci, yayin da kasar ke kokarin ci gaba da samun bunkasuwa mai dorewa da kara zurfa yin gyare-gyare.
Mataimakin babban darekta na daya na asusun David Lipton wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, bayan da asusun ya wallafa wata kasidar shekara-shekara game da yanayin tattalin arzikin kasar Sin, ya ce ana hasashen bunkasuwar kasar Sin a wannan shekara ta 2017 za ta kai kaso 6.7 cikin 100, kamar yadda lamarin yake a shekarar da ta gabata, kana sama da yadda gwamnati ta yi hasashe na kimanin kaso 6.5 cikin 100.(Ibrahim)