Shahararen kamfanin nan na Bloomberg ya bayyana cewa, yanzu haka hankalin masu zuba jari a kasar ta Sin ya karkata ga sunan tambari da fasahar kere-kere maimakon sashen makamashi da kayayyaki. Inda a shekaru goman da suka gabata, kamfanonin kasar Sin suka kashe kimanin dala biliyan 139 wajen sayen albarlkatu a tsoffin kamfanonin makamashi, ko da yake lamarin ya canja a 'yan shekarun nan.
Sai dai wani rahoto na baya-bayan nan da Macro Polo na cibiyar Paulson a jami'ar Chikago ta Amurka ya fitar ya nuna cewa, an samu canji a shekarar 2014, yayin da irin wadannan kamfanoni suka mayar da hankali ga bangaren kere-kere, ciki har da fasahar yanar gizo da manhajoji, kananan na'urorin daidaita wutar lantarki, sadarwa, zirga-zirgar jiragen sama da kayayyakin wutar lantarki, maimakon tsohuwar al'adar zuba jari a bangaren makamashi. (Ibrahim Yaya)