Da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi masa tambaya game da shawarar a lokacin da yake amsa tambayoyi tare da jawabi na shekara shekara a jiya, shugaba Putin ya ce shawarar ta daban ce da ba saba gani ba, sannan tana kunshe da nasarori.
Ya ce abu mafi dacewa da ya kamata a yi shi ne, inganta hadin kai karkashin tsarin kungiyar raya tattalin arzikin nahiyar Turai da Asia da kuma shawarar ziri daya da hanya daya.
Kasar Sin ce ta gabatar da shawarar Ziri daya da hanya daya a shekarar 2013, inda ya kunshi hanyar siliki ta kan tudu da kuma ta cikin ruwa ta karni na 21.
Manufar shawarar ita ce, samar da wata hanya ta cinikayya da kayayyakin more rayuwa da za ta hada yankin Asia da Turai har ma da Afrika, ta yadda zai zarce hanyoyin Siliki na da. (Fa'iza Mustapha)