Yayin wani taron manema labarai a jiya, Najmi Nakoo ya ce hukumomi sun kwace iko da filin jirgin saman kasa da kasa na Tripoli ba tare da sa hannun wata kungiya ba
Kwamandan ya ce dakarun gwamnati sun sake karbe iko da wasu sansanonin soji da wasu wurare dake kudancin Tripoli, wadanda a baya ke hannun kungiyoyin adawa masu dauke da makamai
A ranar 27 ga watan Mayu ne rikici ya barke tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai, inda daya ke mara baya ga gwamnatin hadin kan kasar, yayin da dayar ke goyon bayan hambararriyar gwamnatin Khalifa al-Ghawil, al'amarin da ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce yayi sanadin mutuwar sama da mutane 55 tare da jikkata akalla wasu 100.
Tun a shekarar 2011 ne kasar Libya ke fama da rikici tun bayan boren da ya hambarar da tsohon shugaba Muammar Gaddafi.
Kasar dai na kokarin sauya mulki a lokacin da ake tsaka da fuskantar rarrabuwar kawuna tsakanin jam'iyyun siyasa da kuma mamayar kungiyoyi masu dauke da makamai. (Fa'iza Mustapha)