An samu tashin hankalin ne tsakanin wata kungiyar masu dauke da makamai, wadda ta kulla kawance da gwamnatin hadakar kasar, da wasu dakaru karkashin kungiyar 'Salvation Government'.
A halin da ake ciki, hukumar lafiya ta kasar ta ce har yanzu tana kokarin tantance hakikanin adadin mutanen da suka mutu ko suka ji rauni.
Bayan barkewar rikicin, gwamnatin hadakar kasar ta yi Allah wadai da dakarun kungiyar 'Salvation Government', wadanda a cewarta suka kaddamar da harin ba tare da la'akari da jama'a ba, har ma aka jefa su cikin wani yanayi mai matukar hadari.(Bello Wang)