Bayan kasashen Turkiya, Rasha, Greece, Italiya, Croatia da Cyprus suka tura jiragen saman kashe gobara a yankin, a ranar 25 ga wata kasar Masar da kasar Jordan suka ba da taimako don kashe gobarar ga kasar Isra'ila. Kasar Falasdinu ma ta aike da 'yan kwana kwana da motocin kashe gobara zuwa yankin, haka zalika, jiragen saman kashe gobara masu samfurin Boeing 747 da 'yan kwana kwana da kasar Amurka ta tura sun isa kasar Isra'ila a daren jiya Jumma'a.
A jiya Jumma'a kuma, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, dalilin guda daya da ya haddasa tashin gobara a yankin duwatsu shi ne laifin mutane, ya kuma yi gargadi cewa, kasar Isra'ila za ta gurfanar da wadanda suka aikata laifin tashin gobarar a gaban kuliya, kuma bisa labarin da 'yan sandan kasar suka bayar, an ce, tuni an kama mutane 15 wadanda ake zarginsu da hannu a tashin gobarar. (Maryam)