in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya yi Allah wadai da kudurin Isra'ila na sake gina matsugunan Yahudawa
2017-04-01 12:27:46 cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa tare da yin All..wadai ga kudurin da gwamnatin Isra'ila ta tsai da, na sake gina sabon matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan.

Sanarwar da Guterres ya bayar ta bakin kakakinsa a jiya Juam'a ta bayyana cewa, ya soki daukacin matakan da Isra'ila ta dauka, domin zai yi nakasu ga kokarin da ake na wanzar da zaman lafiya, tare da yin mummunan tasiri ga "shirin kafa kasashe biyu" adaidai lokacin da ake kokarin warware rikici dake tsakanin Isra'ila da Palestinu.

Sanarwar ta jaddada cewa, gina matsugunin ya sabawa dokar kasa da kasa, kuma zai kawo illa ga kokarin na tabbatar da zaman lafiya.

A ranar 30 ga watan Maris ne, majalisar ministocin Isra'ila ta amince da kudurin gina sabon matsugunan Yahudawa a gaabar yammacin kogin Jordan, domin tsugunar da mutanen da za su bar matsugunin Amona da aka gina ba bisa ka'ida ba.

karon farko kenan cikin shekaru sama da 20 da suka gabata, da gwamnatin Isra'ila ta amince da kudurin sake gina matsugunin Yahudawa a yankin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China