A safiyar Lahadi bisa agogon wurin, daga cikin yankin da kasar Sham ta mallaka kan tudun Golan, wasu dakaru sun kai hari ga yankin da sojojin Isra'ila suka mallaka, inda daga cikin makaman da suka yi amfani da su har da karamar igwa. Nan take sojojin Isra'ila sun mayar da martani, kuma sun tura jiragen saman yaki domin yin luguden boma-bomai. Sakamakon dauki-ba-dadi shi ne an lalata motoci da makamai na dakarun, tare da kashe wasu 4 daga cikinsu. Yayin da a bangaren sojojin Isra'ila, babu wanda ya mutu ko kuma ya ji rauni.
A cewar sojojin saman Isra'ila, mutanen 4 mambobi ne na kungiyar Yarmuk Martyrs, wadda ke da alaka da kungiyar IS.(Bello Wang)