in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta zargi Turkiyya da yunkurin haddasa rikici a arewacin kasarta
2017-07-07 10:08:15 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Syria ta zargi gwamnatin Turkiyya da yunkurin haddasa wani sabon rikici a garuruwa dake arewacin kasar Syrian, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar SANA ya rawaito.

Ma'aikatar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta zargi Turkiyyar da yin kutse a garuruwan Azaz da Jibreen dake kusa da arewacin lardin Aleppo.

Sanarwar ta ce wannan sabon yunkuri na yin kutse wani bangare ne da Turkiyyar ke amfani da shi domin haddasa tashin hankali a yankunan Syriar.

Da ma dai gwamnatin Syriar ta jima tana kaiwa MDD korafi kan abin da tace yin kutse da kasar Turkiyyar ke yi mata a wasu yankunanta wadanda ke makwabta tsakanin kasashen biyu.

Syria ta bayyana yunkurin a matsayin laifin da ya keta dokokin kasa da kasa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China