in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Syria ta saki mutane 672 da aka yi garkuwa da su
2017-06-25 13:39:55 cri
Gwamnatin kasar Syria ta sanar cewa, an saki mutane 'yan kasar Syria 672 da aka yi garkuwa da su don kara samun sulhu a tsakanin kabilun kasar.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya bayar, ministan shari'a na kasar Syria Hisham al-Sha'ar ya gana da mutanen da aka sake su a birnin Damascus a wannan rana, tare da yin jawabi, inda ya bayyana cewa, mutanen 672 sun zo ne daga jihohi da dama a kasar Syria, mutane 588 cikinsu ne suka zauna a kurkuku dake Damascus, ciki har da mata 91.

Al-Sha'ar ya bayyana cewa, an saki mutanen ne don nuna kulawa ga jama'a da sa kaimi ga samun sulhu a tsakanin kabilu, da ba su dama don su bada gudummawa ga kasar.

Kungiyar masu adawa ta kasar Syria ta bayyana cewa, bayan da rikicin kasar Syria ya faru, gwamnatin kasar Syria ta yi garkuwa da 'yan kasar fiye da dubu 10, an bukaci gwamnatin kasar da ta sake su. A shekarun baya baya nan, gwamnatin kasar Syria ta saki mutane da dama da aka yi garkuwa da su a wurare daban daban na kasar don sa kaimi ga samun sulhu a tsakanin kabilu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China