Yayin zantawar tasu, Mr. Li Yuanchao ya ce yana fatan bangarorin biyu za su kara amincewa da juna kan harkokin siyasa, da habaka hanyoyin hadin gwiwar moriyar juna a fannonin kudi, da na hada-hadar su, da samar da ababen more rayuwa, da na'urori, da ma'adinai, da makamashi, da kuma aikin gona da na kamun kifi. Kaza lika ya yi fatan za a kara yin musayar al'adu da ta ilmi, domin ciyar da dangantakar sada zumunta dake tsakanin kasashen biyu gaba.
A nasa bangaren, Mr. Bawumia ya bayyana cewa, kasarsa na fatan mayar da martani ga shawarar "ziri daya da hanya daya" karkashin inuwar dandalin hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, domin sada al'ummomin kasashen biyu da tarin alherai. (Sanusi Chen)