Rahotanni na cewa, za a aike da tawagar ne cikin rukunoni biyu, za kuma ta yi aiki na tsawon shekara guda. Kaza lika dakarun za su bar nan kasar Sin nan gaba cikin wannan wata na Mayu.
Dakarun dai na kunshe da sojoji injiniyoi, da dakarun tsaro da na lafiya. Wannan ne dai karo na 5 da kasar Sin za ta aike da dakarun ta na wanzar da zaman lafiya zuwa Mali. (Saminu Hassan)