in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba gudunmuwar dala miliyan 5 ga shirin samar da abinci na WFP domin tallafawa 'yan gudun hijirar Kenya da abinci
2017-06-08 09:55:16 cri
Shirin samar da abinci na MDD wato WFP, ya karbi gudunmuwar dala miliyan 5 daga gwamnatin kasar Sin, domin samar da abinci ga 'yan gudun hijira dake sansanin Kakuma na arewacin Kenya.

An yi amfani da kudin wajen sayen ton 9,000 na kayayyakin abinci ga 'yan gudun hijira 420,000 dake sansanonin 'yan gudun hijirah na Dadaab da Kakuma.

Bayan shafe shekara guda da rage yawan abinci da yake bai wa 'yan gudun hijirar saboda karancin kudi, sabbin gudunmuwa daga kasar Sin da wasu kasashe ya ba shirin WFP damar komawa ba da abinci kamar yadda ya saba, na tsawon watanni 4.

A cewar darkatan shirin WFP a kasar Annalisa Conte, suna maraba da muhimmiyar gudunmuwar da kasar Sin ta ba shirin, a lokacin da yake fafutukar samar da abinci ga 'yan gudun hijira dake sansanoninsu a arewacin Kenya, wadanda ke fama da rashin abinci saboda karancin kudi.

Shi kuwa Jakadan kasar Sin a Kenya Liu Xianfa, cewa ya yi, kasar Sin ta yi gaggawa wajen amsa kiran da aka yi wa kasashen waje da su taimakawa 'yan gudun hijirar.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta bada kayayyakin jin kai ko kuma kudi da ake bukata. A lokaci guda kuma, ta ba da tallafin da za ta iya wajen taimakawa shirye-shiryen da hukumomin daban-daban suka kirkiro, sannan ta bada shawarwari da suka dace. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China